1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ehud Olmert : saban Praministan Isra´ila

April 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2n

Shugaban kasar Isra´ila Moshe Katsav, ya naɗa Ehud Olmert, Praministan riƙwan ƙwarya, a matsayin saban praministan da zai girka gwamnati, bayan nasara da jam´iyar sa, ta Kadima ta samu, a zaɓen yan majalisun dokoki, na ranar 28 ga wata maris da ta wuce.

Tunni Ehud Olmert ya shiga tantanawa da jam´iyun siyasa da zumar girka gwamnatin haɗin kan kasa.

Kamar yada kudin tsarin mulkin ƙasar Isra´ila ya tanada, Ehud Olmert, na da wa´adin kwanaki 28 ,domin girka wannan gwamnati.

A cikin jawabin farko da yayi, bayan naɗin, ya bayyana mahimman batutuwa guda 2, da gwamnatin, zai maida hankali akai.

Wato, batun samar da zaman lahia da Palestinu, sai kuma haɓaka tattalin arzikin ƙasa, da kauttata rayuwar jama´a.

Ehud Olmert ya sanar manema labarai cewa nan da loakci kalilan za shi kammala tantanawa da yan siyasa, ya kuma bayyana sabuwar gwamnatin, da za ta shiga ba da ɓata lokaci ba, ga ayyukan da ke gabanta.