1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan ya gana da Rouhani kan ballewar Kurdawa

Ramatu Garba Baba
October 4, 2017

A wannan Laraba shugabanin kasashen Turkiyya da Iran ke ganawa kan yunkurin ballewar Kurdawa daga gwamnatin Bagadaza a wani al'amari da ake ganin na tattare da hadura na barkewar rikici.

https://p.dw.com/p/2lCp5
Iran Präsident Hassan Rohani & Tayyip Erdogan, Präsident Türkei
Hoto: Reuters/Kayhan Ozer/Presidential Palace

Mahukuntan kasar Turkiyya sun ce sojoji hudu ne suka mutu a wani harin bam da ake zargin 'yan tawayen Kurdawa da kai wa a kudancin kasar. Akwai wasu sojoji hudu da suka samu rauni a harin na wannan Laraba. Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ke ziyara a kasar Iran, inda suka tattauna da takwaransa na Iran Hassan Rouhani kan illolin da ke tattare da yunkurin ballewar Kurdawa daga gwamnatin kasar Iraki da zummar samun 'yancin cin gashin kai a matsayin yankin Kurdawa zalla. Batun da ke  haifar da fargabar ga makomar zaman lafiya a yankunan da ke ci gaba da fama da ayyukan mayakan kungiyar IS.

A baya gwamnatin Turkiyya ta dauki matakan soji na toshe kan iyakarta da yankunan Kurdawan a yunkurin nuna rashin goyon bayan zaben neman ballewar da ya gudana a makon jiya.