1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Erdogan: Za mu kawo karshen yakin Siriya

Yusuf Bala Nayaya
March 30, 2019

Erdogan ya fada wa magoya bayan jam'iyyarsa a birnin Istanbul cewa babu batu na kawar da fadan Siriya a kan takarda za su je filin daga ne a kawo karshensa bayan zaben Lahadi

https://p.dw.com/p/3Fvzu
Türkei Istanbul Hagia Sophia | Wahlplakat Präsident Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Akgul

Shugaba Turkiyya Tayyip Erdogan ya bayyana a wannan Asabar cewa Turkiyya za ta kawo karshen rikicin Siriya a filin daga bayan zaben kananan hukumomi a ranar Lahadi. Erdogan ya fada wa magoya bayan jam'iyyarsa a birnin Istanbul cewa babu batu na kawar da wannan fada na Siriya a kan takarda za su je filin daga ne a kawo karshensa.

Wannan dai na zama wani mataki na kara koda jam'iyyarsa ta AKP don kara samun goyon baya yayin zaben.

Turkiyya dai ta kai farmaki ga Kurdawa sau biyu bayan ratsa iyaka inda ta shiga Siriya ta kuma yi barazanar kara kai farmaki muddin ba a dena barazana ga iyakarta ba.