1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ernst Nolte masanin tarihin Jamus ya rasu

Abdourahamane HassaneAugust 18, 2016

Allah ya yi wa shahararan masanin tarihin nan na Jamus, Ernst Nolte rasuwa a Berlin.

https://p.dw.com/p/1Jl3K
Ernst Nolte Historiker
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Puchner

Nolte wanda ke daya daga cikin masanan tarhin kasar ta Jamus wanda ya yi suna sossai ya kasance mafi yin kwankwanto, kana mafi haddasa sabannin ra'ayoyi a tsakanin hakidoji a cikin rubuce-rubucen da ya rika yi.

A shekara ta 1980 ya rubuta wani litafi mai sunan a bin da ya wuce wanda kuma bai son ya wuce,Wanda ya janyo muhawara mai zafi a tsakanin masana tarihin kasar da aka kira yakin masana. A cikin litafin da ya wallafa Nolte ya nuna banbanci da ke tsakanin hakidar Nazis da Communist. Nolte wanda aka haifa a Witten a yammacin Jamus ya rasu yana da shekaru 93.

.