1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Etienne Tshisekedi ya koma gida Kwango

Mouhamadou Awal BalarabeJuly 28, 2016

Madagun 'yan adawan Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ya na shirin taka rawa a siyasar kasarsa bayan shekaru biyu na rashin lafiya. Saboda haka ne ya koma gida.

https://p.dw.com/p/1JWyQ
Kongos Tschisekedi ist nach Kinshasa zurückgekehrt
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P Photo/J. Bompengo

Madugun 'yan adawa Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ya koma gida bayan da ya shafe shekaru biyu a Beljium don nemen magani. Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce dangane da shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa . Shi dai Etienne Tshisekedi ya samu kyakkyawar tariya daga dubban magoya bayansa a Kinshasa babban birnin kasar.

'Yan adawa na zargin shugaba kabila da jan kafa wajen shirya sabon zaben shugaban kasa da nufin ci gaba da dawwama a kan karagar mulkin. Joseph Kabila zai kammala wa'adinsa na biyu a karshen wannan shekarar. Sai dai gwamnatinsa ta bayyana cewar matsalar karancin kudi da rashin kayan aiki na barazana ga shirya sahihin zabe. lamarin da wani dan adawa Kwango ya ce ba za ta sabu ba.

"Ba ma so Kabila ya tsawaita wa'adinsa na mulki. So muke yi ya mutunta kundin tsarin mulki ta hanyar shirya mana zabe a kan kari. Idan ko bai yi ba, to za mi dauki Tshisekedi a matsayin shugaba da zai yi rikon kwarya kafi shirya sabon zabe."