1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU da Birtaniya sun fara tattaunawa

June 19, 2017

Yayin da Birtaniya ta fara tattaunawa da EU kan ficewa daga kungiyar, jami'in EU Michel Barnier yace wajibi ne a shawo kan batutuwa masu sarkakakiya.

https://p.dw.com/p/2exhU
Brexit Verhandlungen beginnen in Brüssel Barnier mit Davis
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Jagoran tattaunawar kungiyar EU Michel Barnier da takwaransa na Britaniya David Davis sun shedawa manema labarai cewa sun shirya tattaunawar don shata yadda Britaniya za ta fice daga kungiyar baki daya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Firaiministar Britaniyan Theresa May ta rasa gagarumar rinjaye da take da shi a majalisar dokokin kasar al'amarin da ake ganin zai iya haifarwa kasar tarnaki a tattaunawar.

Al'ummar Britaniya dai sun zabi ficewa daga kungiyar EU a zaben raba gardama da aka yi a bara.