1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na kokarin bin sahun Amirka

August 15, 2014

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU na duba yiwuwar tura tallafin makamai zuwa kasar Iraqi domin taimakawa dakarun kasar da na Kurdawa su fatattaki 'yan ta'addan IS.

https://p.dw.com/p/1CvN2
Hoto: Reuters

Yanzu haka dai ministocin harkokin kasashen ketare na kungiyar ta Tarayyar Turai na can na gudanar da taro a birnin Brussels domin duba yiwuwar amincewa da tura makamai ga kurdawan kasar Iraqin da ke yakar 'yan kungiyar ta'addan IS. Tuni dai kasashen Birtaniya da Faransa suka amince da tura makaman ga dakarun Iraqi da kuma na Kurdawan, sai dai kuma ministan harkokin kasashen ketare na Faransa Laurent Fabius ya ce akwai bukatar sauran kasashen kungiyar ta EU suma su amince da kai agajain makaman ga dakarun gwamnati da kuma na Kurdawan Iraqin. Ita ma dai kasar Italiya da a yanzu haka ke jagorantar shugabancin kungiyar ta Tarayyar Turai ta nunar da cewa Kurdawan kasar Iraqi na bukatar taimakon kungiyar. Dama dai tuni Amirka ta fara yin ruwan bama-bamai ta sama a yankunan da 'yan ta'addan suka mamaye, baya ga tallafawa sojojin Iraqin da na Kurdawa domin su yaki 'yan ta'addan ta kasa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar