1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU na tunanin kafa wata runduna

Abdourahamane HassaneDecember 15, 2015

Kwamitin Ƙungiyar Tarrayar Turai ya gabatar da buƙatar kafa wata runduna ta gadin iyakokin nahiyar Turai da kuma gaɓar teku.

https://p.dw.com/p/1HNtt
EU Passkontrollen Grenze zwischen Frankreich und Belgien
Hoto: Reuters/P. Rossignol

Rundunar za ta kula da tsaron iyakokin nahiyar Turai da kuma gaɓar tekun inda har an amince da shawarar.Ƙungiyar ta Eu ta ce kusan mutane miliyan ɗaya da rabi suka tsallaka kan iyakokin na Turai ba kan ƙaida ba tun farkon watan Janeru na wannan shekara akasarinsu 'yan ciranin waɗanda ba a yin rejistansu ba.

Abin da ya sa wasu ƙasashen kamar su Jamus da Austriya tuni suka soma gudanar da bincike na wucin gadi a kan iyakokinsu.