1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU: Sharrudda kan shiga yaki da IS a Libiya

Ahmed SalisuFebruary 21, 2016

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ba za ta shiga yaki da 'yan kungiyar nan ta IS a Libya ba muddin ba ta samu goron gayyata daga sahihiyar gwamnatin kasar ba.

https://p.dw.com/p/1HzJ3
Libyen Kämpfer GNC gegen IS
Hoto: Getty Images/AFP/M.Turkia

Kantomar hulda da kasashen ketare ta EU din Federica Mogherini ce ta ambata hakan a wata hira da wata jaridar kasar Faransa ta yi da ita aka kuma fidda ta a wannan Lahadin.

Mogherini ta ce abu ne mai wuya iya kawar da kungiyar daga Libya din ba tare da cikakken goyon baya na halastaciyyar gwamnati a kasar ba don haka EU ba za ta tsoma bakinta kan wannan batu.

Amirka da sauran kasashe dai sun dau lokaci su na kokari na kawar da kungiyar ta IS a akasar ta Libya wadda ke fama da rikici na shugabanci tun bayan da aka hambarar da gwamnatin Mua'ammar Ghaddafi a shakara ta 2011.