1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin binciken 'yan gudun hijira

Yusuf BalaDecember 16, 2015

A cewar hukumar kasar ta Italiya ya zame mata dole ta dauki matakan doka masu tsauri wajen tattara wadannan bayanai.

https://p.dw.com/p/1HNzU
Italien Flüchtlinge in Lampedusa
'Yan gudun hijira a ItaliyaHoto: Reuters/A. Bianchi

Hukumar kungiyar Tarayyar Turai a ranar Talata ta bukaci mahukunta akasar Italiya su yi amfani da karfi wajen tattara bayanai na hotunan yatsu ga baki dayan sabbin 'yan gudun hijira a kasar, bayan da ta samu kasar da laifi na rashin tattara bayanan cikin rumbun ajiyar bayanai na kasashen na EU.

A cewar hukumar kasar ta Italiya ya zame mata dole ta dauki matakan doka masu tsauri wajen tattara wadannan bayanai na 'yan gudun hijirar ko da kuwa zai sanya a tsare wadanda suka ki yarda a dauki hotunan yatsunsu tsawon lokaci. A cewar kalaman na hukumar ya zama dole a tabbatar da tattara bayanan yatsu na bakin hauren dari bisa dari ba tare da bata lokaci ba.

Ministan harkokin cikin gida a kasar ta Italiya Angelino Alfano a jiya Talata ya ce da ma tsarin dokar kasar ta Italiya ya amince da amfani da karfin sai dai 'yan majalisa na sake nazari kan wannan bukata.

A ranar Alhamis ne dai babban taron na EU zai tattauna kan sabon shiri me cike da takaddama wanda zai bayyana a wannan mako, shirin da zai ba wa jami'an tsaro dama a kan iyaka su kutsa kai cikin wata kasa da ke karkashin kungiyar ba tare da sani mahukuntanta ba.