1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta cimma matsaya kan bakin haure

June 29, 2018

Kasashen Turai sun cimma matsaya dangane da matsalar nan ta bakin haure wadda ke ci masu tuwo a kwarya.

https://p.dw.com/p/30WBi
Belgien - EU-Gipfel in Brüssel - Merkel
Hoto: picture alliance/dpa/AP/G. Vanden Wijngaert

Shugabannin kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai sun cimma matsaya dangane da batun nan na bakin haure, bayan daukar tsawon daren Juma'a suna turance juna a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

Shugaban majalisar Tarayyar ta Turai Donald Tusk ne ya sanar da labarin a wannan Juma'a.

Manyan jami'an diflomasiyyar kungiyar sun tabo batun wuraren kafa sansanonin bakin hauren, sai dai ba su fayyace lamarin da dalla-dalla ba.

Yanzu dai abin da ya fito fili shi ne duk wata kasar da ke cikin wannan kungiya, na iya tsara tare da karbar bakin da ma masu neman mafaka cikin kasashen na su, yadda suka gani ya dace suka kuma amince da shi.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce tana da kwarin gwiwar cewa kungiyar ta EU za ta ci gaba da warware matsalolin da suka danganci bakin da ke kutsawa ba tare da sun sami amincewar hukumomi ba.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya yaba nasarar da aka samu, yana mai cewa a karshe dai nasarar ta EU ce.