1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kakaba wa Iran karin takunkumi

December 23, 2012

A wani mataki na hana wa Iran ci gaba da shirinta na nukila kungiyar Tarayyar Turai(EU) ta dora mata karin takunkumi

https://p.dw.com/p/178Ae
Hoto: aeoi.org.ir

Wannan takunkumi ya hada ne da haramcin sayar wa kasar ta Iran kayan kera jiragen ruwa da wasu karafa da fasahar aikin man fetur da Kompyutoci na aikin masana'antu . Bugu da kari kungiyar ta dakatar da sayen iskar gaz daga kasar ta Iran. Ta kuma yi bayani game da yadda za a rinka sa ido akan harkar tura kudade zuwa bankuna daga Iran. An kuma dora haramcin yin wata harka ta kudi tsakanin bankunan Turai da ma'aikatun kudin Iran.

Shugaba Mahmud Ahmedinejad a nasa bangaren cewa yayi kasarsa ta shiga yakin tattalin arziki da abokan gaba. Ya kara da cewa gwamnatinsa ta magance tasirin haramcin sayar da mai da ka dora wa kasarsa kuma sabanin yadda aka zata daga ketare babu wani radadi da Iran ta fuskanta a sakamakon haka. To sai dai duk da haka, takunkumin ya yi mumunan tasiri akan al'umar kasar. Kasashen yamma na zargin Iran ne da kera makaman kare dangi a asirce-zargin da ita Iran din ta musunta.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru-Danladi Aliyu