1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta shiga tsaka mai wuya bayan kammala zabenta

May 27, 2019

Manyan jam’iyyu a zaben majalisar dokokin Turai sun fuskanci koma baya da ke iya zama kalubale, yayin da sauran jam’iyyun suka sami tagomashi. An dai sami fitowar masu kada kuri’a da ba a ga irinsa ba a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/3J9km
Belgien EU Halbmastbeflaggung Anschlag in Nizza
Hoto: Reuters/F. Lenoir

Jam'iyyu masu tsananin kishin kasa da masu kyamar baki da kuma masu fafutukar kare muhalli, sun bai wa masu matsakaicin ra'ayi da hadin kan Turai mamaki a zabukan 'yan majalisar dokokin Turan da aka kammala a ranar Lahadi.

Sakamakon farko dai da aka samu a zaben, na cewa a dole masu rajin ganin an sami hadin kan na Turai su nemi kulla sabon kawance.

Sai dai masu matsakaicin ra'ayin da suka hada da European People's Party da gungun 'yan Social Democrats, da za su rasa rinjaye a majlisar mai kujeru 751, na jayayya da kulla kawance da masu tsananin ra'ayin kishin kasa.