1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da tallafa wa 'yan gudun hijira a Turkiyya

Binta Aliyu Zurmi MAB
March 25, 2021

Shugabannin Kungiyar tarayyar Turai sun shirya daidaita alakarsu da Turkiyya don cimma yarjejeniyar kan 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/3r82r
Hoher Vertreter der EU für Außen- und Sicherheitspolitik Josep Borrel
Hoto: JOHN THYS/POOL/AFP/Getty Images

A taron da suka gudanar shugabannin sun ce abu mafi mahimmanci a wannan lokaci shi ne dafa wa Turkiyya domin ta ci gaba da kula da dubban 'yan gudun hijirar da ke jibge a kasarta maimakon yi mata baraza da matakin kakaba mata takunkumi.

Yanzu haka EU ta sha alwashin farfado da tsohuwar jarjejeniyar da suka cimma a shekarar 2016, yarjejeniyar da ta dakile tururuwar da 'yan gudun hijirar kasar Siriya ke yi a gabar tekun kasar Girka.

Babban jami'in harkokin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce ya zama wajibi EU  ta ci gaba da ba wa Turkiyya zunzurutun kudi har yuro biliyan shida domin ci gaba da kula da 'yan gudun hijirar da ke jibge a kasarta.