1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta yi taro kan rikicin Masar

August 19, 2013

Kungiyar Tarayyar Turai ta EU za ta gudanar da wani taro a ranar Laraba mai zuwa don duba halin da Masar ta shiga tun bayan da soji su ka hambarar da gwamnatin Mursi.

https://p.dw.com/p/19SRO
European Union flag at the Mirador de San Vicente in Rio Madrid, Spain, April 2011. (Photo by Cristina Arias/Cover/Getty Images)
Friedensnobelpreis EU Europäische Union SymbolbildHoto: Getty Images

Ministocin harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ta EU za su gudanar da wani taro ranar Laraba mai zuwa a birnin Brussel na kasar Belgium domin duba hanyoyin da za su bi wajen matsawa mahukuntan Masar Lamba na su warware zanga-zangar da magoya bayan jam'iyyar 'yan uwa Musulmi ke cigaba da yi cikin ruwan sanyi.

Yayin wannan ganawa da ministocin za su yi dai ana sa ran za su yanke shawarar dakatar da bada tallafi da kuma bashin da kungiyar ta yi alkawarin baiwa Masar din wanda yawansa ya kai dalar Amirka miliyan dubu bakwai.

Baya ga wannan batu, a hannu guda akwai yiwuwar sanyawa Masar din takunkumi kan makamai kamar dai yadda guda daga cikin jami'ain kungiyar ta EU Bernardino Leon ya shaidawa manema labarai.

To sai dai duk da wannan, Leon ya ce Turai na ganin cewar har yanzu amfani da matakai na siyasa ka iya kaiwa ga warware dambarwar da Masar din ta shiga tun bayan da soji suka hambarar da gwamantin Muhammad Mursi a cikin watan Yulin da ya gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal