1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗi tashin harkokin siyasa a Afrika ta Kudu

Ibrahim SaniDecember 20, 2007
https://p.dw.com/p/CeIl

Mr Jacob Zuma ya ƙarbi madafun ikon Jam´iyyar ANC a Afrika ta Kudu, kwanaki biyu bayan lashe zaɓen shugaban Jam´iyyar. A jawabin sa na farko, Mr Zuma ya buƙaci haɗin kai a tsakanin ´ya´yan Jam´iyyar ta ANC, don samun sukunin cimma burin da aka sa a gaba. Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya kuma yi alƙawarin yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shugaba Thabo Mbeki. A waje ɗaya kuma babban mai gabatar da ƙara a Afrika ta Kudu ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da zargin cin hanci da rashawa da akewa Mr Zuma. Mr Mokotedi Mpshe ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za su haifar da gurfanar da Mr Zuma a gaban ƙuliya, dangane da zarge-zargen cin hancin da rashawa.