1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanonin China sun yi wa Facebook kutse

Abdourahamane Hassane
June 6, 2018

Kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewar wasu rukunin kamfanoni na Telecom na China wadanda suka hada da Huawei sun yi masa kutse don tsasar wasu bayanai na ma'abuta shafin.

https://p.dw.com/p/2z3R9
Symbolbild Hate Speech
Hoto: DW/P. Böll

Kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewar wasu rukunin kamfanoni na Telecom na China wadanda suka hada da Huawei sun yi masa kutse don tatsar wasu bayanai na ma'abuta shafin. Wannan shi ne karo na biyu ke'nan da Facebook ke samun kansa cikin irin wannan hali bayan abin kunyar da ya faru na wani kamfanin Cambridge na Birtaniya watau Analytica wanda  ake zargi da tattara bayyanai na ma'abuta shafin na facebook kusan dubU 87  don jirgita ra'ayoyinsu.