1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yankin Dafur lamura na kara tabarbarewa

Yusuf BalaJune 30, 2015

A bara Sudan ta bayyana bukatar dakarun sojan kawancen na Afrika da Majalisar Dinkin Duniya su fice daga yankin, bayan zargin dakarun kasar da yi wa mata fyade.

https://p.dw.com/p/1Fpw5
Südsudan UN-Camp in Bor
Hoto: AFP/Getty Images

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin shekara daya ga dakarun wanzar da zaman lafiya da ke aiki a yankin Dafur a yammacin Sudan. Wani abu da ke nuna fatali da kiran da gwamnatin yankin ta yi na a kwashe wadannan dakaru.

Jami'an kwamitin sulhun dai sun bayyana cewa akwai ci gaban dagulewar lamura a wannan yanki, yayin da fada ke kara kazanta tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye.

Tun dai bayan da aka bankado wata badakala ta cin zarafin mata ta hanyar aikata fyade da ake zargin wasu dakarun kasar ta Sudan da aikatawa a garin Tabit, wannan ya sanya mahukuntan na Sudan bayyana bukatar dakarun sojan kawancen na Afrika da Majalisar Dinkin Duniya su fice daga kasar a shekarar bara.

Ana dai ci gaba da neman hanyoyi da za su kai ga damke shugaba Omar Hassan al-Bashir da kotun da ke hukunta manyan laifuka ta ICC ke nema ruwa a jallo bisa laifin kisan kiyashi da haddasa yakin basasa.