1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faduwar farashin na zama kalubale ga OPEC

Arne Lichtenberg/ Usman Shehu UsmanNovember 27, 2014

Samun faduwar farashin man fetir a kasuwannin duniya ya jefa kasashen kungiyar OPEC musamman wadanda suka dogara kacokan kan samun kudin shiga ta wannan fanni shiga rudani.

https://p.dw.com/p/1Duf6
OPEC Fahne Logo
Hoto: picture-alliance/dpa

Dama dai an kafa kungiyar OPEC a shekara ta 1960 domin daidaita farashin danyen mai a duniya. Kasashen da ke cikin kungiyar ta OPEC dai 12 da suka hada da Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait da Katar da Najeriya da Iran da Iraki sai kuma Libiya da Aljeriya da Equado da Venezuela. Wadannan kasashen su ne ke samar da sama da daya bisa uku na yawan danyen mai da ake fitarwa a duniya. Su ne kuma ke da mai da ke shinfide mafiya girma a duniya. Leon Leschus, masani ne kan harkar tattalin arzikin karkashin kasa ya yi tsokaci kamar haka:

"Saudiyya ita ce kasar da tafi fidda danyen mai a kungiyar OPEC. Don haka bayan wargejewar kasar Libiya, Saudiyya ta bunkasa man da ta kan fitar. Don haka idan aka samu faduwar farashim mai a duniya kamar yadda aka gani a baya, to kasashe kamar Saudiyya za su gwammace su bunkasa man da suke sayarwa, a maimakon rage farashinsa".

Ko da yake wasu kasashen nan masu cewa matsalar fidda danyen mai a kasuwannin duniya yana tattare da siyasar duniya da ta kasashen waje, kana da matsaloli na cikin gida. Amma a gefe guda akwai matsin lamba daga kasashe da ke sayen danyen man. Ga irin misalin da masanin Leschus ya bayar.

Iran Erdöl Öl Industrie Raffinerie Arbeiter
Hoto: AP

"Akwai gefe guda na kasar Amirka wadda ke matsawa sai a fara yin amfani da man fetur da ake samu daga sinadarin cikin duwatsu. Wanda kuma a zahiri mai ne da ke da matukar tsada in an kwatanta shi da wanda ake hakowa a karkashin kasa. Wasu na ganin Saudiyya da Amirka suna aiki tare wato sun hada baki ne, domin su karya lagwan kasar Rasha wanda ita ma ke da arzikin mai. Domin kowa ya san cewa Rasha ta dogara matuka daga kudin da take samu a wajen sayar da mai"

Shi ma dai Faran Umbach daraktan cibiyar makamashi da tsaro a jami'ar Kings College da ke London, ya ce babu dayan biyu rigimar da ake yi tsakanin Rasha da kasashen yamma na cikin abinda ke rikita kasuwar danyen mai a duniya.

Venezuela Treffen zwischen Präsident Nicolas Maduro und Opposition in Caracas
Hoto: Reuters

"Idan aka tuna can bayan a shekara ta 1986 farashin danyen mai ya fadi da kashi 50 cikin dari. Tabbas a wacan lokacin Saudiyya da Amirka sun hada baki don karya tattalin arzikin Tarayyar Soviert."

Masanan dai sun bayyana cewa tashin hankali da ake samu a kasar Ukraine wanda ya kai ga aza wa Rasha takunkumi, da kuma rikicin kasashen Siriya da Iraki ya shafi farashin mai a duniya. Wata babbar matsala ita ce kasashe kamar Najeriya da Venezuela da Iraki, suna fidda danyen mai a duniya ba kakkautawa, ba tare da yin ajiyarsa ba.