1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma Francis ya yi kiran da a zauna lafiya

Abdourahamane Hassane
April 28, 2017

Fafaroma Francis ya bayyana haka ne a Masar inda ya soma yin wata ziyara a yau ta kwanaki biyu.

https://p.dw.com/p/2c5S9
Ägypten Besuch vom Papst Franziskus in Kairo
Hoto: Reuters/Egypt TV

Ziyarar wacce ta kwanaki biyu ce na zuwa ne daf da lokacin da kasar take cikin wani hali na dokar ta baci, bayan tagwayen hare- hare da Kungiyar IS  ta kai a kan Kiristoci Kibdawa a farkon wannan wata wanda a ciki mutane 45 suka mutu. Yanzu haka hukumomi a kasar ta Masar sun karfafa tsaro a ko'ina domin kiyaye afkuwar wasu hare-hare.