1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafatawa da masu zanga-zanga a Hong Kong

September 28, 2014

Masu zanga-zanga a Hong Kong sunyi kane-kane a wani mahimmin titi, abun da ya haddasa matsalolin zirga-zirga a wannan birni, tare da arangama da 'yan sanda.

https://p.dw.com/p/1DMKF
Hoto: Reuters

Al'ammura sun tsaya cik a birnin, inda a wannan Lahadin jami'yan tsaro na 'yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa hawaye, ga dubunnan masu zanga-zangar neman girka Dimokradiya, da suka ce babu gudu ba ja da baya a kokowar da suke, wajan ganin sun samu karin walwala ta siyasa, daga hukumomin Chine.

Masu zanga-zangar dai sun cika wata mahimmiyar hanya ce dake tsakiyar birnin, abun da ya haddasa matsalolin zirga-zirga, inda jami'yan tsaron na 'yan sanda sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu zanga-zangar yanayin da ba'a cika samun sa ba a Hong Kong.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu