1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafatawar karshe a zaben Laberiya

Salissou Boukari RGB
October 20, 2017

Hukumar zaben Laberiya ta sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar na makon jiya ta kuma sanar da cewa a ranar bakwai ga watan gobe za a fafata a tsakanin 'yan takara biyu dake neman kujerar shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/2mFpE
Liberia Wahlkampf
Hoto: Reuters/T. Gouegnon

Hukumar zaben kasar Laberiya ta sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar da ya gudana na ranar 10 ga watan Oktoba, inda a yanzu ta tabbata cewa 'yan takara biyu da suka hada da Sanata George Weah tsohon gwarzon dan kwallon kafa na Afirka, da kuma Joseph Boakai dan takarar jam'iyya mai mulki kuma mataimakin shugaban kasar ta Liberiya za su fafata a zagaye na biyu na zaben da zai gudana a ranar bakwai ga watan Nuwamba mai zuwa. A sakamakon karshen da hukumar zaben kasar ta Laberiya ta bayar ya nuna cewa George Weah na kan gaba da kusan kashi 39 cikin 100, yayin da Joseph Boakai ya samu kusan kashi 29 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada. Shugaban hukumar zaben kasar Laberiya Jerome Korkoya ya tabbatar da sakamakon karshe na zaben yayin wani taron manema labarai a birnin na Monrovia:

 Magoya bayan jam'iyyar Congress for Democratic Change  (CDC) ta Sanata George Weah sun  gunadar da bukukuwa a hedkwatar jam'iyyoyinsu  a Monrovia babban birnin kasar, inda suke ganin cewa akwai yuyuwar wanda ya taba lashe kyautar hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA Ballon d'Or na Afrika ya maye gurbin Ellen Johnson Sirleaf wanda  ita ta samu kyautar zaman lafiya a Nobel. Sai dai masu lura da al'amuran siyasa sun kalli lamarin zaben na Laberiya a matsayin wani abun koyi ganin yadda shugabar kasar mai mulki ta ki saka bakinta cikin lamarin. Wani babban abun da ake gani dai a matsayin ci gaban da aka samu, shi ne yadda 'yan kasar ta Laberiya suka bayar da hadin kai ga hukumar zaben kasar, da kuma yadda ita kanta hukumar zaben ta tsaya tsayin daka na ganin ta shirya sahihin zabe.