1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar ceto 'yan matan Chibok

July 14, 2014

Shugaban Najeriya ya sha alwashin ceto 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace tare kuma da ganawa da iyayensu nan ba da jimawa ba.

https://p.dw.com/p/1CceQ
Hoto: Reuters

Mai fafutukar kare 'yancin ilimin yara mata 'yar kasar Pakistan din nan Malala Yousafzai da a yanzu haka take ziyara a Tarayyar Najeriya ta gana da shugaban kasar Goodluck Jonathan kan batun 'yan makarantar sakandaren garin Chibok na jihar Borno da 'yan Boko Haram suka sace. Malala dai na yin bikin cikarta shekaru 17 ne a Najeriyar inda ta ce ta yi hakan ne domin ta nuna damuwarta da kuma niyyarta ta ci gaba da yin fafutukar ganin an sako wadannan 'yan mata da suka kwashe kusan watanni uku a hannun 'yan ta'addan na Boko Haram. Da take jawabi a yayin taron manema labarai da ta gudanar bayan kammala ganawarta da Shugaba Jonathan, Malala ta ce ganawar ta su ta yi armashi domin kuwa ya yi mata alkawarin ganin an sako 'yan matan nan ba da jimawa ba. Malala ta kuma ce shugaban ya dauki alkawarin ganawa da iyayen yaran kamar yadda ta bukata tana mai cewa.

"Na gana da iyayen yaran kuma sun bayyana min damuwarsu ina iya ganin hawaye a idonsu, sun bukaci ganawa da shugaban kasa kuma na bukaci hakan daga gareshi yayin ganawarmu ya kuma yi min alkawarin cewa zai gana da su domin kwantar musu da hankulansu"

'Yar gwagwarmayar dai ta ce fatan da take da shi, shi ne shugaban kasar ya cika wadannan alkawuran biyu kuma za ta ci gaba da yin fafutuka da lakabin "Bring back our girls" har sai ta ga an sako 'yan matan sun koma gaban iyayensu da kuma makarantunsu ba tare da wani cikas ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal