1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar kawar da cutar Polio a duniya

October 24, 2012

Ƙasashen Afghanistan da Pakistan da kuma Najeriya na zaman ƙasashen da su ka rage da alamun cutar shan inna kuma su na ta faɗi-tashi wajen kawar da ita.

https://p.dw.com/p/16ViR
Hoto: picture-alliance/dpa

Kusan kashi hamsin cikin ɗari na yaran da rahotanni su ka nuna cewar an same su da wannan cuta ta Polio sun fito ne daga tarayyar Najeriya kuma galibinsu daga arewacin ƙasar su ke, wajen da cin hanci da rashawa gami da ƙin amincewa da gudanar da rigakafin cutar ke yin zagon ƙasa wajen kawar da ita.

Shugabannin addinai da shugabannin al'umma musamman ma sarakunan gargajiya na nuna matuƙar damuwarsu game da wannan batu.

Dr. Umaru Pate na sashen nazarin aikin jarida a jami'ar Maiduguri ta jihar Borno da ke arewacin Najeriyar na daga cikin mutanen da su ka kewaye Najeriya domin gudanar da nazari kan yadda cutar ta ke a ƙasar.

Dr. Pate ya ce 'mun ga mutanen da zan iya cewa sun kasu kashi biyu. Kashi na farko dai su ne wanda saboda dalilan da su ka haɗa da yanayin wajensu ko kuma wanda za a iya kaiwa gare su amma kuma an kasa yin haka saboda wasu dalilai wanda a iya cewa ƙalubale ne. Kashi na biyu kuwa su ne su ne wanda ke zaune a a cikin birane amma kaiwa gare su na da matuƙar wuya saboda ɗabi'ar da su ka ɗauka ta ƙin amincewa a yi wa yaransu rigakafin cutar'.

To baya ga wannan batun, magana ta rashin tsaro da ke a arewacin na Najeriya musamman ma dai tada ƙayar baya ta masu kaifin kishin addini da ke gwagwarmaya da makamai na taimakawa wajen bawa cutar sararin cigaba da baje kolinta.

Nigeria Boko Haram Anschlag
Tashin hankali na taimawa wajen cigaba da yaɗuwar Polio a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa

Ko a makonni biyun da su ka gabata sai da wasu 'yansanda biyu da su ke wa masu rigakafin Polio rakiya a Kano su ka gamu da ajainsu bayan da wasu mutane su ka bindige su.

Wata matsala har wa yau ita ce isasshen ilimi na yanayin wajen musamman ma dai ta hanyar amfani da taswira wajen kaiwa ga wasu yankuna da kuma rashin watadar waje mai sanyi na adawa alluran, lamarin da Oliver Rosenbauer, kakakin shirin hukumar lafiya ta duniya na yaƙin da cutar ta Polio ya ce wata babbar ƙafar ungulu ce ga yaƙar cutar.

Mr. Rosenbauer ya ce 'a Najeriya batsalar ba ta wuce ta yin kyakkyawan tsari ba abin da na ke nufi shi ne ba a shirya gangamin wayar da kan mutane kan rigakafin cutar yadda ya kamata. Ga misali tara daga cikin yara goma na kamuwa da cutar ce saboda wannan matsala ya yin da cikon na goman ke gamuwa da ita sakamakon ƙin amincewar da iyaye ke yi na yi wa yaransu ragakafin Polio ɗin'.

Wannan cuta dai ta Polio duk da cewar masana kiwon lafiya sun ce ta fi kama yaran da shekarunsu ba su kai biyar ba, bincike ya nuna cewar ta na kama wanda su ka ɗara shekaru biyar da haihuwa. Cutar dai a halin yanzu na zaman barazana tsakanin al'umma a Najeriya da ke da yaran da yawansu ya kai miliyan hamsin. Wannan dalili ne ma ya sanya malamin addinin musuluncin da ke Kano Dr. Ameen Al-Deen Abubakar ya tashi tsaye wajen faɗakarwa a wani mataki na bada gudumawarsa wajen yaƙar cutar.

Poliobekämpfung Nordnigeria
Shugabanin al'umma na ta yin kira wajen amincewa da rigakafin PolioHoto: Thomas Kruchem

Shehin malamin 'ya ce ni jagora ne na al'umma saboda haka ya kyautu in taimakawa mutane. Daga cikin bincike da na gudanar na gano cewar na da wuyar warkara wata sa'ar ma ta kan kai ga kashe yaro saboda haka ina goyan bayan yi wa yara rigakafin cutar domin kuwa hakan bai da wata illa'.

Daga watan Satumban bana zuwa yau dai yara sha uku ne aka gano sun kamu da wannan cuta ta Polio, abin jira dai yanzu shi ne haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen ganin an ci nasarar kawar da cutar a arewacin Najeriya wanda abu ne mai yiwuwa kamar yadda hukumar lafiya ta nunar inda ta bada misali da ƙasar Indiya wadda tuni ta kawar da ita.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu