1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasdinawa sun samu nasara a MDD

Usman Shehu UsmanSeptember 11, 2015

Da gagarumin rinjaye kwamitin sulhu na MDD ya amince wa Falasdinawa da su kafa tutarsu a majalisar a wani abu dake zama babbar nasara bisa dadadden yunkurinsu na samun kasa mai yancin kai

https://p.dw.com/p/1G2LP
Palästinensische Flagge am UNESCO-Hauptquartier
Hoto: picture-alliance/dpa/I. Langsdon

Kasashe 119 suka kada kuri'ar amincewa Falasdinawan, su kafa tutuar tasu, yayinda kasashe bakwai kacal suka jefa kuri'ar kin amincewa, ciki kuwa harda Isra'ila da Amirka. A yanzu hakan 'yankin Falasdinu da fadar Vatikan, sune kadai kasashen da ke da tuta na 'yan kallo da ba cikakkakun mambobi a majalisar. A ranar 30 ga watan da muke ciki ne shugaban Falsdinawa Mahmud Abbas, zai daga tutar Falasdinawan a MDD bayan jawabin da zai yi wa zauren. Isra'ila dai ta soki matakin da aka dauka na barin Falsdinawa su kafafa tuta, domin hakan ya nuna duniya na kan hanya da basu yanci a matsayin kasa baki daya, inda tuni a yanzu Falasdinawa ke da kujera a UNESCO da kotun MDD da ke hukunta manyan laifuka a birnin Hague.