1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa da Libya sun sanya hannu kan kwangiloli na biliyoyin daloli

December 11, 2007
https://p.dw.com/p/Ca0N

Ƙasasahen Faransa da Libya sun rattaba hannu kann wasu kwangiloli da ƙudinsu ya tasamma euro biliyan 10 a ranar farko ta ziyarar shugaba Muammar Ghaddafi zuwa Faransa.Wata sanarwa da ofishin shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ta fitar ta baiyana cewa kwangilolin sun haɗa da sayarda jiragen saman fasinja guda 21 ga Libya tare kuma da yarjejeniyar haɗin kai kan a fannin makamashin nukiliya.Sarkozy shine shugaban wata ƙasa ta yamma na farko da ya karɓi baƙuncin Ghaddafi tun lokacin da ya ɗauki alkawarin watsad da aiyukan tarzoma da dakatar da yunkurinsa na neman mallakar makaman nukiliya shekaru 4 da suka shige. Har ya zuwa wancan lokaci an maida kasar ta Libya saniyar ware cikin alummomin duniya na tsawon shekaru da dama.