1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa na rufe sansanin Calais

October 24, 2016

Hukumomin kasar Fasaransa sun fara aikin kwashe 'yan gudun hijira 'yan share wuri zauna da ke sansanin Calais da aka fi sani da "Jungle Camp" wanda ke kusa da tashar jirgin kasa a bakin ruwa.

https://p.dw.com/p/2RbYj
Frankreich Räumung Dschungel von Calais
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Morenatti

A yanzu dai an girke jami'an tsaro kusan 1,250 da manyan motoci da za su kwashe bakin haure kusan dubu 8,000 izuwa sassa daban daban na kasar ta Faransa. To sai dai wasu daga cikin mazauna sansanin na Calais na ganin matakin da gwamnati ta dauka na murkushe mazaunin da suka shafe sama da shekara guda a matsayin rashin tausayi da jinkai. Mafi akasarin mazauna sansanin dai 'yan kasashen Afganistan ne da kuma Iritiriya da 'yan kasar Sudan da ke da niyar ketarawa nahiyar Turai.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hukumomin Faransa ke yunkurin rufe sansanin ba, amma 'yan gudun hijiran ke sake tarewa a ciki. Wannan karon dai gwamnatin Faransa ta dau matakin rufe sansanin na Calais ne har abada da nufin samun saukin tashin tashina tsakanin jami'an 'yan sanda da bakin hauren da ke makalewa man'yan motoci dan tsallakwa zuwa Turai.