1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona na barazana ga zabe a Faransa

June 28, 2020

A wannan Lahadin ce ake gudanar da zabukan magadan gari da shugabannin kananan hukumomi gami da kansiloli a kasar Faransa.

https://p.dw.com/p/3eSgR
Frankreich Präsident Emmanuel Macron
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Zaben da ke gudana a garuruwa dubu biyar a cikin kasar ya fuskanci koma-baya, bayan an yi zaben farko a watan Maris a sakamakon bazuwar cutar corona. Annobar coronavirus ce ta sa aka jirkinta zagaye na biyu na zaben zuwa wannan Lahadi. 

Hukumomi sun ce dole ne kowa ya sanya takunkumi a rumfar zabe. Kazalika wajibi ne a bar tazara a tsakanin masu kada kuri'a, sannan kuma an ajiye sabulun wanke hannu a rumfunan zabe, duka dai a mataki na takaita yaduwar wannan ciwo. Sai dai kuma duk da haka ana zullumin jama'a ba za ta fito ba sosai a saboda fargabar da al'umma ke da ita ta kamuwa da annobar Covid-19. 

Faransa dai na cikin kasashen gaba-gaba da corona ta yi wa barna, inda kawo yanzu cutar ta hallaka mutum dubu 30.