1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ce a sake zama kan Boko Haram

Salissou BoukariMay 15, 2015

A lokacin da ya gana da takwaran aikinsa na Chadi a birnin Paris, shugaban Faransa Francois Hollande ya bukaci a sake shirya taron kasa-kasa kan yaki da Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1FPzP
Francois Hollande
Francois HollandeHoto: Reuters/G. Fuentes

Shugaban na ChadiDeby Itano ya ce lalle an karya lagwon kungiyar Boko Haram, amma kuma mayakanta na nan a warwatse kuma suna hare-haren sari ka noke. Shugaban na Faransa ya nemi kasashen da ke da hannu cikin yakin da ake da Boko Haram su sake wani zama don ganin abubuwan da za su iya yi tare.

Ya yin wata ziyara da ya kai a birnin Abuja na Tarayyar Najeriya a farkon wannan makon, Shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ba'a samun hadin kai tsakanin sojojinsu da na Najeriya duk kuwa da cewa sojojin nasu na yakin ne cikin kasar ta Najeriya.