1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ci Google tarar euro miliyan 500

Abdullahi Tanko Bala
July 13, 2021

Kamfanin Google ya ce ba a yi la'kari da kokarinsa na yin sulhu ba, a tarar da aka yi masa. Kamfanin dai na da wa'adin watanni biyu ya gabatar da jadawalin biyan diyya ga kamfanonin dillancin labarai.

https://p.dw.com/p/3wQnA
Google-Logo
Hoto: picture alliance / Geisler-Fotopress

Hukumar sa ido kan fasahar mallaka da gogayyar kasuwanci ta Faransa ta ci tarar kamfanin Google euro miliyan 500 saboda rashin nuna adalci a shawarwai da kamfanoni dillancin labarai da kamfanin na Google ke amfani da labaransu sannan kuma da saba ka'ida kamar yadda yake kunshe a dokokin hakkin mallaka na kungiyar tarayyar Turai.

Wannan dai ita ce ta tara mafi girma da hukumar sa ido kan gogayyar kasuwanci ta dora wa wani kamfani da ya saba hukuncinta kamar yadda shugabar hukumar Isabelle De Silva ta shaidawa manema labarai tana mai cewa hukuncin ya yi daidai da girman laifin da kamfanin na Google ya aikata.

Hukumar ta kuma bukaci kamfanin Google ya gabatar wa kamfanonin dillancin labaran wani tayin karin tagomashi kan fasaharsu da yake amfani da su a yanzu ko kuma ya fuskanci karin tara da zai kai euro 900,000 a kowace rana.

Wani mai magana da yawun kamfanin na Google a cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin larabai na AFP ya baiyana hukuncin da cewa abin takaici ne kwarai.