1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu

Mohammad Nasiru AwalSeptember 10, 2015

Firaministan Faransa ya yi kira ga EU da ta goyi bayan kafa tutar Falasdinu a shalkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York.

https://p.dw.com/p/1GUmB
Frankreich Paris Saint Quentin Fallavier Anschlag Gasfabrik Manuel Valls
Manuel Valls Firaministan FaransaHoto: Getty Images/AFP/A. Jocard

Firaministan Faransa Manuel Valls da takwaran aikinsa na Falasdinu sun jagoranci taron hadin guiwa na farko na gwamnatocinsu a birnin Paris, sa'o'i kalilan gabanin wata kuri'ar da za a kada a Majalisar Dinkin Duniya kan amincewa da kafa tutar Falasdinu a cibiyar majalisar da ke birnin New York. Firaministocin biyu sun sanya hannu kan jerin yarjeniyoyin hadin kan siyasa, tattalin arziki da kuma al'adu. Lokacin da yake magana bayan ratabba hannu, Firamistan Faransa Manuel Valls ya ce kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan kafa kasar Falasdinu.

"Faransa za ta ci gaba mara wa yunkurin kafa kasar Falasdinu. A cikin 'yan makonni masu zuwa za mu ba wa ma'aikatar kudin Falasdinu Euro miliyan takwas baya ga wasu miliyan takwas da muka ba ta cikin watan Yuni."

Kawo yanzu ana nuna rashin tabbas a kan matsayin kasasahen kungiyar EU masu ra'ayoyi mabanbanta game da kafa tutar Falasdinu a shalkwatar ta Majalisar Dinkin Duniya. Amirka da Isra'ila na adawa da wannan kudiri.