Faransa ta sanar da jadawalin janye sojojinta daga Mali
March 7, 2013A cikin jawabin da ya yi yayin ziyarsara a birnin Warsaw na kasar Poland, Hollande yac e sojojin za su kwashe watan Maris suna gudanar da aiki a kasar ta yammacin Afirka. A wancan wata na Fabarairu ministan harkokin wajen kasar ta Faransa, Laurent Fabius ya ce daga watan Maris ne sojojin za su fara ficewa daga Mali. Shugaba Hollande ya kira aikin da sojojin ke yi a Mali tamkar wani muhhimmin mataki wajen yaki da taaddanci. Su dai yan kishin Islamar an samu nasarsar fatattakarsu daga manyan biranen dake Arewacin kasar, to amma su kan shiga yin aratabun da ba a rasa ba a yankin Ifogha. Yayin ziyara tasa a birnin Warsaw, Hollande ya kuma tattauna tare da shugabar gwamnatim Jamus, Angela Merkel da shugabannin kasashen Poland da Hungary da Cek da Slovakia inda suka mai da hankali ga bukatar karfafa yin hadin-gwiwa a fannin tsaro.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar