Faransa ta yaba da zaɓen Mali
July 29, 2013Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault ya jinjinawa ƙasar Mali da ta iya ta gudanar da abin da ya kira zaɓe mai nasara musamman ma ga Faransa wadda ta tura dakarunta ƙasar suka tasa ƙeyar ƙungiyoyin masu kaifin kishin addini.
Lokacin wata ziyara da ya kai ƙasar Malaysia Firaminista Ayrault ya aikawa mahukuntar ƙasar gaisuwar taya murnarsa, ya kuma ce nasarar zaɓen ya ɗaga ƙimar Faransa a idon duniya, musamman ga waɗanda suka ƙyamace ta saboda rawar da taka a lokacin da ƙasar ta Malin ta shiga mawuyacin hali sakamakon juyin mulki da rikicin da ya biyo baya.
Kawo yanzu dai ba a fitar da sakamakon zaɓen a hukumance ba, to sai dai shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande ya ce yana farin cikin ganin an gudanar da zaɓen ba tare da wata gagarumar matsala ko tashe-tashen hankula ba.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi