1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ba ta son jinkirta ficewar Birtaniya

Binta Aliyu Zurmi
September 8, 2019

Ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a yau Lahadi ya yi watsi da yunkurin neman jinkirta ficewar ki  Birtaniya daga kungiyar tarayyar Turai da aka tsara za ta fice a karshen watan Octoba da ke tafe.

https://p.dw.com/p/3PFlK
Jean Yves Le Drian Verteidigungsminister Frankreich
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Camus

A cewar Ministan ba za su amince da kwan-gaba-kwan-baya da ake yi a duk watanni uku kan wannan maganar ba. Ya kara da cewa hakurin Faransa a kan wannan batu ya fara kaiwa makura.

Le Drain ya ce ya kamata Firai Minista Boris Johnson ya fiddo da mafita musamman ma akan batun iyaka da Jamhuriyar Ireland.

Sau biyu Birtaniya na samun karin wa'adi daga kungiyar tarayyar Turai kan shirin ficewar, wanda ada aka tsara a karshen watan Maris din da ya gabata.

Yanzu haka dai Birtaniya na shirin tatara inata-inata daga kungiyar a karshen watan Octoba, wanda Mr Johnson yai alkawarin ficewar kasar ko da yarjejeniya ko babu.

A makon da ya gabata Firai Ministan ya yi ikirarin cewa ya gwammace mutuwarsa akan ya nemi karin wa'adi kan ficewar Birtaniyar daga EU.