1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Yiwuwar kai harin ta'addanci

Gazali Abdou TasawaMay 31, 2016

Amirka ta gargadi kasar Faransa da kan hadarin da ke akwai na na kai harin ta'addanci a lokacin gasar cin kofin kwallon kafa na kasashenTurai a Faransa cikin watan Yuni.

https://p.dw.com/p/1IxxC
Frankreich Fußball Stade de France
Hoto: picture alliance/Sven Simon

A cikin wata takardar da ofishin sakataran harakokin wajen Amirka ya fitar kan batun hadarin da ke tattare da yin balaguro a kasashen Turai, ya ce filayen da za a buga wasannin ko kuma wuraren da za a nunasu a Faransa dama a sauran kasashen Turai wurare ne masu hadarin fuskantar hare-haren ta'addancin.

Ofishin sakataran harakokin wajen Amirkar ya gargadi Amirkawa masu tafiya yawon buda ido ko halartar wasu taruka a kasashen na Turai da su kaurace wa shiga wuraren shakatawa da gidajen cin abinci ko manyan shagunan sayar da kaya dama tashoshin sufuri na safa-safa da jiragen kasa. Kazalika Amirka ta ce akwai irin wannan barazana a gasar tsereren kekuna ta Tour de France da Faransar za ta shirya a cikin watan Yuli mai zuwa.