Gwamnatin Faransa ta dauki matakin faranta wa 'yan sanda
December 19, 2018Talla
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da wasu kungiyoyin 'yan sandan kasar suka sanar da shirinsu na janyewa daga bakin aiki don gudanar da zanga-zanga kan wasu bukatu da suka hada da karancin ma'aikata da batun kasafin kudi.
Har ya zuwa wannan lokaci babu tabbacin amincewa da wannan tayi daga bangaren 'yan sandan kasar ta Faransa. Koda yake za a gudanar da wani taro tsakanin ministan harkokin cikin gida da kuma wakilan kungiyar 'yan sanda a wannan Larabar bayan da kungiyar 'yan sandan ta rabawa manema labarai wata sanarwa inda suka baiyana cewar sun fi karfin a siyo su da kudi.