1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta taimaka wa Lebanon da makamai

December 29, 2013

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce zai taimaka wa da sojin Lebanon da makamai idan Lebanon ta buƙaci Faransa ta yi hakan.

https://p.dw.com/p/1AiIX
Shugaba Farncois Hollande na FaransaHoto: Reuters/Laurent Dubrule

Hollande ya bayyana hakan ne a yau bayan da ya yi wata ziyara da ya kai Saudi Arabiya inda ya ƙara da cewar Faransa ta yanke shawarar yin hakan ne domin ganin Lebanon ɗin ta tsaurara matakan tsaronta daidai lokacin da ƙasar ke fama da tashe-tashen hankula da ke da nasaba da yaƙin basasa ke ci gaba da wakana a ƙasar Siriya da ke makobtaka da ita.

Gabannin wanan alwashi da Faransa ta sha dai, Saudi Arabiya ta bayyana cewar za ta taimaka wa da Lebanon ɗin da tsabar kuɗi dalar Amirka miliyan dubu uku don ƙara ƙarfin sojinta, inda masarautar Saudin ta ce ta yi hakan ne a ƙokarinta na ganin yankin Gabas ta Tsakiya ya samu dawammamen zaman lafiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: AbdourahAmane Hassane