1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa za ta tsaurara matakan zaman baki

Gazali Abdou Tasawa
July 12, 2017

Faransa ta sanar da shirin gina cibiyoyi dubu bakwai da 500 na tsugunnar da masu neman takardun zaman kasa da kuma wasu dubu biyar ga 'yan gudun hijira nan zuwa shekara ta 2019.

https://p.dw.com/p/2gP7X
Paris Migranten Eiffelturm
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Widak

Faransa ta sanar da shirin gina cibiyoyi dubu bakwai da 500 na tsugunnar da masu neman takardun zaman kasa da kuma wasu dubu biyar ga 'yan gudun hijira nan zuwa shekara ta 2019.  Firaministan kasar ta Faransa Edourd Philippe ne ya sanar da hakan a wannan Laraba.

Kazalika firaministan ya ce za a rage wa'adin gyaran takardun masu neman izinin zaman kasa daga watanni 14 zuwa shida. Gwamnatin Faransar ta ce ta dauki wannan mataki ne domin gaggauta tantance 'yan gudun hijira na gaske da wadanda ke zuwa da nufin neman kudi kawai a Faransar, kana ba za ta yi sassauci ba ga mutanen da za a yi watsi da takardun nasu wajen korarsu daga cikin kasar.

A shekara ta 2016 daga cikin baki dubu 91 da aka kama a kasar, dubu 31 ne aka bai wa umurnin ficewa daga cikin ta, amma dubu 25 ne kawai suka yarda suka fice.