1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransawa sun kada kuri'ar zaben shugaban kasa

Yusuf Bala Nayaya
April 23, 2017

Marine Le Pen ta jam'iyyar masu kin baki da mai sassaucin ra'ayi Emmanuel Macron na cikin 'yan takara sha daya da ake musu kallon 'yan gaba cikin wadanda ake sa ran su kai ga zagaye na biyu a zaben shugaban Faransa.

https://p.dw.com/p/2bkjD
Frankreich Präsidentschaftswahl
Hoto: Getty Images/AFP/F. Florin

Al'ummar Faransa sun fita kada kuri'a karkashin matakai na tsaro a zagayen farko na zaben da ke zama da wuya a bayyana inda ya dosa, wanda kuma sakamakonsa ke zama mai muhimmanci idan ana magana ta sanin inda Kungiyar Tarayyar Turai ta sanya gabanta. An bude tashoshin kada kuri'ar da misalin karfe takwas shida kenan agogon GMT.

Marine Le Pen ta jam'iyyar masu kin baki da mai sassaucin ra'ayi Emmanuel Macron cikin 'yan takara sha daya ana musu kallon 'yan gaba cikin wadanda ake sa ran su kai ga zagaye na biyu a zaben a ranar bakwai ga watan Mayu duk da kasancewar rabuwar kai tsakanin masu zabe a dangane da 'yan takarar da za su zaba.

Irin ba zata da karbuwar masu adawa da baki da ta kai Donald Trump ga fadar White House da ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU na cikin abin da ke ba wa Le Pen  'yar shekaru 48 kwarin gwiwa, yayin da shi kuma Macron dan shekaru 39 ya tasamma zama shugaba na Faransa mafi kankantar shekaru da manufoifinsa na ci gaba da zaman kasar a Tarayyar Turai da bunkasar tattalin arziki ke ba shi karfin gwiwa.