1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fararen hula na cikin kunci a birnin Mosul

November 3, 2016

Yayin da sojojin Iraqi da mayakan Kurdawa ke ci gaba da yiwa yankin birnin Mosul kawanya, kungiyoyin agaji sun bukaci samun damar kwashe dubban fararen hula a sansanin 'yan gudun hijira na Khazer da ke arewacin Iraqi.

https://p.dw.com/p/2S73h
Irak Flüchtlinge 27.07.2014
Hoto: Getty Images/Afp/Safin Hamed

Babu abin da ka ke gani a sansanin sai bakin hayaki da ya turnuke sararin samaniya dubban jama'a maza da mata da yara kanana suka nemi mafaka a sansanin wanda ke tazarar kilomita 40 daga gabashin Mosul, bayan da suka yi kaura daga yankunan su bayan da sojojin Iraqi suka kaddamar da luguden wuta a kan kuniyar IS da ke rike da birnin Mosul. Hotunan talabijin sun nuna yadda mutanen suke zaune a laka sakamakon ruwan sama da ya jika turbaya a hanyar da ke tsakanin tantunan kamar yadda wata mai suna Rafi ta bayyana halin fargabar da suke ciki:

"Muna zaune a cikin tabo da ruwan sama, babu abin da za ka iya samu ka saya, bamu da suturu babu komai, tsawon kwana hudu ina fama da ciwon kai, bani da ko da kofin shayi da zan sha."

A gefe guda wasu yara suna kokarin debo ruwa daga wani katon dakin ajiyar kayayyaki suna zubawa a cikin kwalbar roba. Duk da tsananin sanyi suna sanye da gajeren wando da takalmi fade. Mutane kimanin dubu 20.000 ne suka yi kaura daga gidajensu makonni biyu da suka wuce tun bayan kaddamar da gagarumin farmakin akan yan IS. sun gudu domin kaucewa musayar wutar tsakanin sojojin kawance da ke yakar yan IS da magoya bayansu. Yan IS din sune ke iko da kusan daukacin birnin na Mosul. Mutane kusan miliyan daya da rabi ne ke zaune a birnin.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi ragistar dubban daruruwan yan gudun hijirar a yankunan da ke hannun 'yan IS kafin kaddamar da wannan farmakin na 'yantar da birnin. A yanzu haka dai kusan babu kowa a sansanin 'yan gudun hijirar da ke arewacin Iraqi, haka kuma ana fama da karancin abinci da sauran kayayyakin bukatu. Da hannu wasu yara suke haka rami domin sanya turakun tantunan da iyayensu ke ciki don kara karfafa shi. A cikin tantunan dai yan katifu ne kalilan da yan kayayyakin yara rataye a kan igiya.