1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cafke wasu da ake zargi da harin Turkiya

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 14, 2016

Jami'an 'yan sandan Turkiya sun cafke wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a kitsa harin da aka kai birnin Santanbul´na kasar.

https://p.dw.com/p/1Hcnp
'Yan sanda na farautar maharan Turkiya
'Yan sanda na farautar maharan TurkiyaHoto: picture-alliance/dpa/P. Kneffel

A wannan Larabar Firaministan Turkiyan Ahmet Davutoglu ya sanar da cafke wasu mutanen hudu wanda ya kawo adadin wadanda jami'an 'yan sanda ke tsare da su zuwa mutane biyar. Ana dai zargin wani haifaffen kasar Saudiya da ke da alaka da kungiyar IS mai kimanin shekaru 27 a duniya da kai harin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10 Jamusawa tare da raunata wasu da dama. Tuni dai ministan harkokin cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere ya ziyarci birnin na Santanbul domin ganewa idanunsa halin da ake ciki.