1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farautar masu kaifin kishin addini a Gao

February 13, 2013

Sojojin kawance na Mali da Faransa na shiga gida gida domin kame masu kaifin kishin addini da ke boye a birnin Gao da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/17djF
Hoto: picture-alliance/dpa

Sojojin Faransa da na Mali na ci gaba da daukan matakan zagulo masu kaifin kishin addini daga inda suke boye a birnin Gao da ke arewacin kasar. Wasu mazauna garin sun baiyana cewa sojojin kawance na shiga gida gida a wasu sassa na Gao domin gudanar da bincike. Wadanda suka shaidar da lamarin suka ce dakarun sun kame masu kaifin kishin addinin da dama.

Rundunar sojojin Faransa ta yi nasarar kwance kilogram 600 na kullin sinadarorin hada bama-bamai da ta gano a wani gida da ke kusa da hotel da 'yan jarida na kasasheh ketare ke da zama. Ana kyautata zaton cewa masu kaifin kishin addinin ne suka dana wannan kullli na bam. Ko da a makon da ya gabata, sai da suka kaddamar da hare-haren kunar bakin wake guda biyu.

Makwanin da suka gabata ne sojojin Mali da na Faransa suka kubutar da birnin na Gao daga hannun masu kaifin kishin addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal