1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faretin 'yan luwadi da madigo a Kolon

Yusuf Ibrahim JarbagaJuly 6, 2016

Masu fafutukar auren jinsi na kasashe dabam-dabam sun yi amfani da gangaminsu wajen neman a sakar musu marar auren jinsi wato namiji ya auri namiji mace ta auri mace.

https://p.dw.com/p/1JK76
Hoto: DW/F. Taube

Masu fafutukar samun dauwamammen 'yancin auren jinsi tsakaninsu sun ta rera baitoci dangane da 'yancin da suke da shi kamar sauran al'umma gami da yin jawabai dabam-dabam.

Daya daga cikinsu ya ce: "Muna wannan gangami ne don mu nemi hukumomi su yi mana adalci na bamu dama mu yi abin da 'yancinmu ya bamu. A bar mace ta auri 'yar uwarta mace, shi ma namiji a barshi ya auri namiji ba tareda an tauye musu 'yancin su ba, saboda haka mun zo ne don mu gana da junannmu kuma mu karewa junan mu 'yanci."

Dangane da abin da ya faru ga yan'uwansu 'yan luwadi da madigo wadanda wani dan bindaga ya bude wa wuta a Orlando da ke Amirka, sun bayyana damuwarsu game da juyayin wannan rana.

Köln Christopher Street Day 2016
Tutar masu neman jinsi ta yi ta kadawa a KölnHoto: DW/F. Taube

Shi dai wannan taro ya samu halatar masu fafutukar 'yancinsu daga wurare dabam-dabam, don haka ne ya sa DW ta ji ta bakin Philip wanda ya ce ya halarci taron ne don ya samu 'yancinsa ganin inda ya fito yana fuskantar wariya kamar yadda ya bayyana

Ya ce: "Ina jin dadin rayuwata da abokin ma'amalata wanda shi ma namiji ne. Sai dai matsalar wani lokacin samun abokin ma'amala namiji a kauyikan Jamus abu ne mai wahala saboda kamar ba su yarda da abin ba. Amma anan Cologne ana samu sosai mutane sun amince da yin hakan saboda ba wani abin gudu ba ne, al´ada ce."

Ita kuma Meriya na daga cikin matan da ke da wannan ra'ayi ta bayyana cewa:"Ni kowa nawane, ina ma'amala da mace inta samu kuma ina ma'amala da namiji saboda ni na dade ina haka. Amma iyayena ba sa son hakan."

Wasu kasashe sun amince 'yan fafutukar su yi auren jinsi daya ciki har da nan Jamus, yayin da wasu kuma ke tir da hakan.