1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba a sansanonin 'yan gudun hijira a Najeriya

Kamaluddeen SaniFebruary 12, 2016

Fargaba na cigaba da karuwa a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabashin Najeriya bayan harin da aka kai sansanin 'yan gudun hijirar da ke Dikwa a jihar Borno.

https://p.dw.com/p/1HtwE
Nigeria,Yola Malkohi Flüchtlingscamp
Hoto: DW/Jan-Philipp Scholz

Hankulan 'yan gudun hijira dubai ne da ke sansanonin 'yan gudun hijira a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ne dai suka tashi sakamakon kaddamar da harin kunar bakin wake da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke a garin Dikwa cikin jihar Borno wanda ya yi sanadiyar hallaka sama da mutane hamsin a yayin da karin saba'in suka jikkata.

Lamarin dai na zuwa ne bayan da ministan tsaron Najeriya Janar Mansur Dan Ali Mairitaya ya yi gargadin cewar:

''Sansanonin ‘yan gudun hijira a shiyyar Arewa maso gabashin Kasar na fuskantar barazanar kai hare-haren na ‘yan kunar bakin wake da ke sajewa da ‘yan gudun hijira.''

Rundunar sojin Najeriyar dai tace yanzu haka maharan na yin amfani da wata dabara domin sajewa da 'yan gudun hiijra a sansanoni da hakan ke cigaba da zama babbar matsala mai daure kai ga mutanen da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijirar.

Wani da ke zama dan gudun hijira a daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira a Yola jihar Adamawa da ita ma ke fusakantar hare-haren kunar bakin waken ya shaida wa tashar DW cewar:

"Yanzu haka yana gudun hijira a Yola amma sakamakon harin garin Dikwa al'amarin ya firgita shi matika,irin hare-haren nan na rasa halin da na nake ciki yanzu, akai mana tsaro a garuruwan mu mu komawa muke son yi, a garin mu kowa ya san kowa zamu iya tantance bako a cikinmu."

Nigeria,Yola Malkohi Flüchtlingscamp Bild 8
Hoto: DW/Jan-Philipp Scholz

Koda a 'yan kwanakin baya ma dai sai da 'yan kunar bakin waken suka kutsa cikin sansanonin 'yan gudun hijirar a jihohin Adamawa da Borno dukkanin su da ke Arewa maso Gabashin Najeriya tare da hallaka mutane da dama.

To sai dai yayin da wannan fargaba ke karuwa, Muhammad Kanar da ke zaman jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA:

Ya ce: "Su dai jami'an tsaro da ke aiki a wuraren da ake da sansanonin 'yan gudun hijira na bakin kokarinsu wajen tabbatar da tsaro ga mazauna sansanonin 'yan gudun hijira kana kuma gwamnatin jihar Bono ta na bamu tallafi na killace sansanonin wanda tuni aiki ne da ya riga yayi nisa."