1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaban yan Mali da ke zaune a Faransa

January 23, 2013

Dangane da yaƙin da ake yi a ƙasar wanda ke barazana ga tsaron lafiyar sauran jama'ar ƙasar Mali

https://p.dw.com/p/17QUI
--- 2013_01_14_Mali_Seperationsbewegung.psd

Kimani yan ƙasar Mali kamar mutun dubu ɗari ne ne suke zaune a ƙasar Faransa kuma tun lokacin da aka fara yin tashin hankali a kasar suke lura sau daƙafa dangane da abinda ke faruwa

A garin Montreuil inda yan Malin suka kai dubu shida ,yan Malin sun gudanar da wani taro na musammun jama'a jigim suka taru a wani tsohon gida wanda ba shi da wutar lantarki tsakiyar gidan kuma an mayar da ita kasuwa inda wasu yan Mali ke saye da sa yerwa.Wata mata mai sayar da shinkafa da miyar mafe irin ta babanrawa ta riƙa tattaunawa da jama'ar wanda ta ke baiyana abubuwan da ke kan tebrin abinci na sayar wa.

Galibi dai a irni waɗannan wurare baƙi ya asilin Malin suke dibar girki bayan an dawo daga ƙwadogo, to amma a yau ko da za a sha darmoson to kam sai an kammala taron da yan asilin ƙasar suka kira domin yin nazari akan halin da a ke ciki.

Yan Malin na cikin zaman zulumi saboda rashin samun labarin dangin su

Ko da shi ke ma sojojin Malin yanzu haka suna samun goyon bayan sojojin ƙasar Faransa da na ƙasashen yammancin Afirka domin fatatakar yan tawaye amma yan Malin da ke a Faransa suna cikin fargaba a Bkan sauran dangin su da ke gida Mariam Guineo .Ta ce ''a waya talho ko mun buga ba ma iya samun su da wannan haraka ta yan ta'ada ta ce ko kudi muka aika a kwai wahala kafin su samu domin ba a samun wanda zai je ya ɗauko kudin kowa na jin tsoro''.

Fluchtpunkt Mali: Junge Malier auf dem Sprung nach Europa Typische Tee-Runde in Bamako Zulieferer: Alexander Göbel Cell: +49-(0)-173-734-4060 Home: +49-(0)-228-249-6946 Schumannstr.40 D-53113 Bonn alexgoebel@yahoo.com
Birnin BamakoHoto: DW

Tsokacin yan Mali a kan Amurka da ba ta aika sojin ba a Mali

Faransa dai ta na da sojoji sama da dubu ɗaya a Malin yayin da sauran ƙasashen Afirka suka yi cikaro cikaro suka taimaka da sojoji waɗanda yawan su zai ya kaiwa dubu ukku kana ƙasashen Jamus da Ingila da Amurka suka ba da ta su gundun mowa.Musa Diakite shi ne mataimakin sghugaban ƙungiyar ta yan Mali a garin Montreuil.Ya ce ''ni abin da ban ganeba a yanzu yaƙi ne ake yi da ta'adanci;ya ce ko ba haka ba, ya ce Amurkawa kuma na yaƙi da ta'adanci a duniya baki ɗaya ya ce domin ba zasu isa a Mali ba''

Fluchtpunkt Mali: Junge Malier auf dem Sprung nach Europa Typische Tee-Runde in Bamako Zulieferer: Alexander Göbel Cell: +49-(0)-173-734-4060 Home: +49-(0)-228-249-6946 Schumannstr.40 D-53113 Bonn alexgoebel@yahoo.com
jama'a a garin BamakoHoto: DW

Ko ma dai mi ake ciki a yanzu za a iya cewar hankali ya fara kwantawa a Mali bayan da sojojin Faransa da ke dafa wa dakarun Malin baya suka sake kwato yankunan da yan tawayen suka mamaye tun a cikin watan Maris na shekara bara.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe