1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar ƙasashen duniya a kan yaƙin Mali

December 11, 2012

Yanzu haka har an raɗa suna ga rundunar dakarun ƙasa da ƙasa na nahiyar Afirka wacce za ta ba da ɗauki ga sojojin Mali domin sake kwato yanki arewacin ƙasar.

https://p.dw.com/p/16zuj
Hoto: Habibou Kouyate/AFP/GettyImages

Rundunar wacce ake kira da suna AFISMA har ya zuwa yanzu ba a san ranar da za ta fara aiki ba ,saboda kuwa ɗari ɗarin da MDD ta ke yi na ƙaddamar da yaƙin a arewacin Mali.

Babban abinda MDD ta ke ganin ita ce hanya mafi sauƙi ga warwware rikicin na Mali shi ne na mayar da hankali akan yunƙurrin diflomsiya da farko,domin samun daidaito tsakanin gwamnatin da yan tawayen a kan tashin hankalin wanda ke zaman barazana ga yankin yamancin Afirkan baki ɗaya.

MDD ba ta ba da haɗin kai ba ga rundunar AFISMA

A lokacin da ya ke yin magana a gaban kwamitin sulhu na MDD babban sakataran majalisar Ban Ki Moon ya yi gargaɗin cewar shiga yaƙi na Mali ba tare da amincewar ƙasashen yammancin duniyar ba ,wani babban izgili ne .Ga yaƙin da aka ƙiesta cewar zai iya cin kuɗaɗe kimanin miliyion 500 na Euro ga wanan lokaci da duniya ke fama da fatara da kuma matsalolin na tattalin arziki sannan ya ƙara da cewar.

UN Sicherheitsrat Sitzung
Taron Majalisar Ɗinkin DuniyaHoto: picture alliance/landov

Ya ce ''abu na farko da ke zaman wajibi shi ne tattaunawa ta hanyar shawarwari na siyasa, ya ce haka ya kammata gabannin ɗaukar duk wani matakin soji''.Ba shaka dai manufofin da yan tawayen suka kafe akan su sune na girka yan'tatar ƙasa mai bin tsarin shara'a musulumci a yanki na arewaci Malin , kuma waɗannan yan tawaye suna ɗauke da miayagun makamai da suke riƙe da su waɗanda suka sulale da su a ƙarshen yaƙin Libiya.

Matasin lamba da ga ƙungiyar ECOWAS na ɗaukar matakin sojin

Tun da farko dai ƙungiyar ƙasashen yankin yammacin Afirka ECOWAS ta ba da gudun mowa sojojin karo karo har guda dubu 3300 domin fatatakar yan tawayen.To amma halin da yankin na arewacin Mali ya ke ciki na zaman wani ƙungurimin daji na iya zama babban cikas ga rundunar ta AFISMA ,inda ba ta da goyon bayan ƙasashen yammacin duniyar.Marco Wyss wani ƙwarrare ne akan sha'anin tsaro a wata cibiyar bayar da horo da ke a Zurich.Ya ce ''dajin ya na da girma kuma Mali ƙasa ce mai girma ta fuskar fasali sannan ya ce lokaci shi kan sa ,ya na taka rawa a cikin lamarin

In this still frame made from video provided by ORTM Mali TV, Mali's
Firamista Cheikh Modibo Diarra wanda yayi murabus ba zato ba tsammaniHoto: AP

ya ce makaman soji na ƙasashen ECOWAS da kuma makaman da rundunar ta AFISMA za ta samu ba zasu iya aminta ba; da yanayin na yankin na hamada, shima ya ce wata babbar matsala ce.

Tattaunawa tsakanin 'yan tawaye da gwamnati ta kawo jingiri ga AFISMA

Wan abin da ya kawo jingiri kuma ga rundunar ta AFISMA bayan fargaban da MDD ta ke da shi shi ne amincewar da wasu ɓangarorin yan tawayen guda biyu na Asaradine da MNLA waɗanda suKa amince suka kuma soma tattaunawa da gwamnatin Mali a Burkina Faso a ƙarƙashin jagoranci shugaba Blaise Compaore.To amma duk da haka ƙungiyar ƙasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS na gaggauta buƙatar ganin an ɗauki matakan soji akan yan tawayen.A wata ziyara da ya kai a brnin Paris na Faransa shugaban ƙasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara wanda shi ne shugaban ƙungiyar ta ECOWAS ya buƙaci Faransa da ta ƙara matsa ƙaimi ga kwamitin tsaron na MDD domin rundunar ta fara yaƙi gadan gadan kafin nan da wani lokaci. Ya ce ''tilas ne a ɗauki matakin sojin kana da sauri, ya ce idan kwamitin tsaron na MDD ya amince da ƙudirin a cikin wannan wata muna tsamani nan ,bada ɓata lokaci ba ,za a soma yaƙin kwato arewacin Mali''.

Mali Tuareg Unabhängigkeitsbewegung Mouvement national de libération de l'Azawad MNLA
Dakarun ƙungiyar 'yan tawaye na MNLAHoto: AP

A yanzu za a iya cewar magana ta rage ga MDD kafin ɗaukar matakin wanda ƙasar Faransa ke a sahun gaba wajan ganin hakan ya tabbata, amma sai dai baya ga shakun da MDD ta ke da shi akan yaƙin, haka suma ƙasashe maƙofta irin su Aljeriya da Cadi na da zulumi akan yunƙurin na AFISMA wanda suke gani wata barzana ce ta bazuwar yaƙin a cikin ƙasashen su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal