1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar kasashe kan cutar Ebola.

July 31, 2014

Yaduwar da cutar Ebola ke ci gaba da yi a wasu kasashen Afirka, ya fara haifar da tsoro ga sauran kasashen duniya, inda tuni suka fara daukan matakai.

https://p.dw.com/p/1Cmgu
Hoto: picture-alliance/dpa

Kasar Birtaniya ta nuna damuwarta kan wannan lamari na cutar ta Ebola, yayin da Hong Kong, ta sanar da yiyuwar daukan matakai na kauracewa. Kungiyar likitoci ta duniya ta Médecins sans frontières, ta sanar cewa, wannan kwayar cuta da a halin yanzu ta yi sanadiyar saruwar a kalla mutane 670 a yammacin Afirka, ta fuce matakin da ake tsammani, inda ta ce akwai hadarin nan gaba wasu kasashe su fuskanci bullar wannan cuta.

Ebola dai ta yi kamari ne a kasashen Gini, Laberiya da Saliyo, inda a halin yanzu aka samu mutun guda da ya rasu sakamakon cutar a Tarayyar Najeriya, bayan da ya fito daga kasar Laberiya ta jirgin sama, tare da yada zongo a filin jirgin saman birnin Lome na kasar Togo.Tuni dai shugabar kasar Liberiya ta bada umarnin rufe makarantun kasar baki daya, a wani mataki na neman takaita yaduwar cutar. Sai dai daga nashi bangare masanin kimiyar nan kuma daya daga cikin wadanda suka gano kwayar cutar ta Ebola a shekarar 1976 dan kasar Beljiyum Farfesa Peter Piot, yace da wuya cutar ta bazu a sauran kasashen Turai ko Amirka.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman