1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar komawa gidan jiya a Mozambik

October 25, 2013

Bayan da tsohuwar kungiyar 'yan tawayen Renamo ta yi shelar janyewa daga yarjejeniyar zaman lafiya a Mozambik, an fara nuna fargabar cewa kasar ka iya tsunduma cikin rikici.

https://p.dw.com/p/1A5oW
epa03920680 Military personnel pictured inside the Renamo base in Sadjungira, province of Sofala Province, central Mozambique, 23 October 2013. Government forces on 21 October attacked the base of Mozambique's oppositional Renamo movement leader Afonso Dhlakama and therewith ended an over 20-year-long running peace agreement. EPA/ANDRE CATUEIRA +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Jaridun a wannan makon sun fi mayar da hankali ne a kan rikicin da ya kunno kai a kasar Mozambik. A labarinta da ta rawaito madugan yaki na cewa "shekaru 21 na zaman lafiya ya isa hakan" jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi.

Kasar Mozambik na daya daga cikin kasashen Afirka da ake sa ran za su samu bunkasa. Godiya ta tabbata da arzikin gas, masu zuba na layin samun shiga wannan matalauciyar kasa. Amma tana barazanar fadawa rikici shigen wanda ta yi fama da shi a baya, biyo bayan sanarwar da kungiyar adawa ta Renamo ta bayar cewa ta yi bankwana da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a shekarar 1992, kana ta koma fagen yaki. Renamo wadda bayan kawo karshen yakin basasan kasar ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa ba ta taba zama barazana ga Frelimo mai jan ragamar mulki ba. Shekaru uku da suka wuce karin farashin kaya abinci ya janyo wata zanga-zanga a babban birnin kasar Maputo, wadda aka murkusheta da karfin tuwo. Kuma kusan shekara guda da ta wuce jagoran Renamo Dhlakama ya kafa sabuwar hedkwata a kan tsunukan Gorongosa dake tsakiyar kasa. Sannan a watan Maris na wannan shekara an fara kai hari da makamai a kan matafiya tsakanin Maputo da birnin Beira mai tashar jiragen ruwa. An zargi Renamo da kai hare-haren sannan tun a watan Afrilu an yi fadace-fadace tsakanin magoya bayan Renamo da kuma 'yan sanda.

Gwagwarmayar neman iko ta rikide zuwa yaki

epa03919437 Locals flee Maringue after an attack by gunmen on a local police station in Maringue, central Mozambique, 22 October 2013. The incident came after government forces had reportedly attacked the base of Mozambique's opposition Renamo movement leader Afonso Dhlakama, thereby ending an over 20-year-long running peace agreement. EPA/ANDRE CATUEIRA pixel
Masu tsere daga rikicin MozambikHoto: picture-alliance/dpa

Zaman lafiyar shekaru 20 da aka samu a Mozambik ya ruguje inji jaridar Berliner Zeitung tana mai cewa gwagwarmayar neman madafun iko tsakanin tsohuwar kungiyar 'yan tawaye ta Renamo da jam'iyyar Frelimo dake jan ragamar mulki ta rikide zuwa fada gadan-gadan. Bayan wani farmaki da dakarun gwamnati suka kai kan hedkwatar Renamo dake yankin Gorongosa, tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta ba da sanarwar janyewa daga yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla da jam'iyar Frelimo. Bayan kawo karshen yakin basasan a 1992, al'ummar kasar ta Mozambik su kimanin miliyan 25 sun samu bunkasar tattalin arziki bayan da Frelimo wadda a da ke zaman mai bin tsarin gurguzu ta koma wata jam'iyya mai bin tsarin jari hujja.

Italy/Sicily, Lampedusa - August 20, 2009 About 75 illegal African immigrants have died while travelling on a crowded rubber dinghy between Libya and Italy, Italian media reported. Archive file of a refugee boat at the mercy of the waves near Lampedusa coasts. Keine Weitergabe an Drittverwerter.
'Yan gudun hijira zuwa LampedusaHoto: picture-alliance/ROPI

Kariya ga 'yan gudun hijira na hakika

Bai kamata tekun Bahar Rum ya zama wani babban kabari ba, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali a kan dubban bakin haure dake bi ta wannan hanya mai hadari a kokarin shigowa nahiyar Turai. Bayan sukar manufofin tarayyar Turai da suke zama karfen kafa ga bakin masu neman mafakar siyasa da ingantuwar rayuwa, jaridar kira ta yi tana mai cewa.

"Kamata a samar wa mutanen da ke neman kariya daga gamaiyar kasa da kasa, kyakkyawawan hanyoyin shigowa Turai. Kamata ya yi kuma hukumar tarayyar Turai ta hada kai da babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya domin samun sabbin matsugunai ga wadannan mutane. Ta ce wajibi ne kungiyar EU da kasashen da kawo yanzu ba su da kyakkyawan tsarin ga 'yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa, su shiga cikin shirin samar da sabbin matsugunai. Dole ne a tabbatar cewa 'yan gudun hijira na hakika dake bukatar kariya kamar yara da tsoffi da kuma marasa lafiya a ba su damar shigowa Turai ta kyakkyawawan hanyoyi."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman