1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar sake barkewar yakin basasa a Afirka ta Tsakiya

Gazali Abdou Tasawa MNA
June 9, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargabar yiwuwar sake barkewar yakin basasa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta la'akari da yadda ake samun yawaitar fadace-fadace masu nasaba da kabilanci ko addini.

https://p.dw.com/p/2eQmN
USA UN Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Getty Images/AFP/J. Samad

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana damuwarsa kan halin tabarbarewar zamantakewa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda Majalisar Dinkin Duniyar ke fargabar sake barkewar yaki ta la'akari da yadda ake samun yawaitar fadace-fadace masu nasaba da kabilanci ko kuma addini a makonnin baya bayan nan a kasar, rigingimun da su ne suka haifar da yakin basasa da ya barke a kasar a karshen shekara ta 2013. 

Antonio Guterres ya bayyana wannan damuwa tasa ce a cikin wani rahoton binciken Majalisar Dinkin Duniya kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar inda ya nuna rashin jin dadinsa dangane da hare-haren da ake yawaita kai wa sojojin rundunar Majalisar Dinkin Duniya a yankin Kudu maso Gabashin kasar. Kungiyar Ocha ta bayyana cewa ya zuwa yanzu mutane sama da dubu 500 ne yaki ya tilastawa barin gidajensu a kasar.