1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar yiwuwar hari a Jamus

Pinado Abdu WabaNovember 18, 2015

Bayanan da aka samu daga binciken harin Paris ya nuna cewa mai yiwuwa wannan kason farko ne na jerin hare-haren da kungiyar IS ke shirin kaiwa.

https://p.dw.com/p/1H8cP
Terroralarm Wandsbek Hamburg
Hoto: AP

Ministan harkokin cikin gidan Jamus Thomas de Maziere ya bukaci da a dauki batun tsaro a kasar da gaske. Ministan cikin gidan ya baiyana haka ne a wani taron manema labarai na bazata da aka gudanar a ofishin kula da miyagun laifuka na tarayyar, inda ya ce batun tsaro yanzu ya kasance babban barazana  ga Jamus da ma Turai baki daya

"Barazanar tsaro a Turai da Jamus da gaske ne, ya zuwa yanzu, abin da muka sani dangane da hare-haren Paris, ana zargin kashin farko ne na jerin hare-haren da kungiyar IS ta shirya kaiwa, idan har wannan da gaske ne, wannan ne zai zama karon farko na hare-haren da kungiyar IS ta kitsa a Turai, kuma mai yiwuwa ba zai kasance na karshe ba."

Lokacin da yake nasa jawabin a taron manema labaran, shugaban hukumar kula da miyagun laifuka na tarayyar, Holger Muench ya kara jaddada wannan gargadi da cewa kashi daya cikin uku na 'yan asalin Jamus fiye da 750, wadanda suka shiga kungiyar IS domin yaki a Iraki da Siriya sun dawo, sannan, wadansu bata garin na iya sajewa da 'yan gudun hijira milliyan gudan da Jamus ke sa ran baiwa mafaka a wannan shekarar